Taiwan
Jirgin TransAsia ya yi hadari a Taiwan
Hukumomin Kasar Taiwan sun ce mutane 48 suka mutu sakamakon hadarin jirgin sama na Trans Asia a lokacin da ya je saukar gaggawa. Jirgin mai dauke da mutane 58 ya fadi akan gidaje ne kusa da tashar Magong a tsibirin Penghu.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce akwai mutane 10 da suka tsira da ransu.
Cikin wadanda suka mutu an tantance wasu dalibai da ke karatun likitanci ‘Yan kasar Faransa guda biyu.
Jirgin ya raunata mutane 5 da ke kasa bayan ya fado a saman gidajen da ke kusa da tashar Jirgin sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu