Isa ga babban shafi
Rasha

Ukraine: Rasha ta nuna damuwarta kan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta

Rasha ta ce ta damu matuka dangane da matakin da hukumomin kasar Ukraine suka dauka na kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ‘yan aware da ke dauke da makamai a gabashin kasar.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Rashan ta fitar a wannan talata, ta bayyana cewa matakin kawo karshe tsagaita wutar da Kiev ta yi abu ne da zai iya mayar da hannun agogo baya a daidai lokacin da Moscow ke kokarin shawo kan ‘ya aware domin soma tattaunawar zaman lafiya da Ukraine.

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ne ya sanar da kawo karshen tsagaita wutar, bayan da ya tattauna da hukumomin Rasha wadanda ke da matukar tasiri akan ‘yan awaren, inda ya ce daga yanzu za a yi amfani da karfi ne domin murkushe masu tayar da kayar baya.

Har ila yau matakin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da shugaba Poroshenko ya tattauna da shugabannin kasashen Jamus da Faransa wadanda ke kokarin ganin an cimma maslaha a game da wannan batu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.