Majalisar Dokokin Iraki ta kasa zaben sabon shugaba
A yau talata sabuwar majalisar dokokin kasar Iraki ta soma gudanar da zamanta na farko domin zaben sabon shugabanta, da shugaban kasa da kuma nada sabon firaminista.
Wallafawa ranar:
To dai jim kadan bayan da ‘yan majalisar suka soma zaman ne aka dage shi sakamakon sabanin da ya kunno kai dangane da wanda za’a zaba a matsayin sabon shugaban Majalisar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da firaminista Nuri Al-maliki ke neman samun yardar majalisar domin ci gaba da rike matsayinsa karo na uku.
Yanzu haka dai kasar ta Iraki na a cikin halin yakin basasa ne, sakamakon yadda mayakan jihadi suka kwace garuruwa da dama daga hannun dakarun gwamnati, sannan kuma suka sanar da kafa sabuwar daular musulunci a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu