Mayakan Iraqi sun kashe Jami’an tsaro 22
Dakarun kasar Iraqi sun kaddamar da yaki domin kwato garin Tikrit da ya fada ikon Mayakan da ke yin barazana ga gwamnatin kasar. Rahotanni sun ce Mayakan sun kashe Jami’an tsaro kimanin 22 a wata musayar wuta da suka yi a kusa da Bagadaza a yau Assabar.
Wallafawa ranar:
An yi musayar wuta a cikin garin Tikrit tsakanin Mayakan da dakarun Iraqi.
Yanzu haka kuma akwai jiragen yakin Amurka da suka ke shawagi domin kare tawagar kwarrun kasar da suka je ba dakarun Iraqi horo.
Shugaban mabiya Shi’a a Iraqi Ayatollah Ali al Sistani ya yi kira ga ‘Yan siyasar kasar su kafa gwamnatin hadin kai domin kawo karshen rikicin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu