Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Mayakan Iraqi sun kwace ikon cibiyar hada makamai

Mayaka da ke gwagwarmaya a kasar Iraqi sun kwace ikon wata tsohuwar cibiyar hada makamai masu guba ta tsohon shugaban kasar Saddam Hussian, a ci gaba da mamaye arewacin Iraqi da Mayakan ke yi.

Hayaki na fita a wata Matatar ferir a yankin Baiji a kasar Iraqi da Mayaka suka karbe iko
Hayaki na fita a wata Matatar ferir a yankin Baiji a kasar Iraqi da Mayaka suka karbe iko REUTERS/Social Media Website/Reuters TV
Talla

Yanzu haka kuma Amurka tana shirin aikawa da kwararru kimanin 300 domin ba dakarun Iraqi horo don fattakar Mayakan na Sunni da ke yakin kawo karshen gwamnatin Shi’a a kasar.

Mayakan da ke gwagwarmaya a Iraqi sun karbe ikon cibiyar hada makaman ne da ake kira Al Muthanna ta tsohon Shugaban kasa Saddam Hussain, amma Amurka tana tunanin Mayakan ba zasu iya hada makaman ba saboda tana tunanin sinadarai da kayyakin da ke cikin cibiyar sun tsufa.

Tun a 1980 ne Saddam Hussain ya samar da cibiyar hada makaman masu guba, kuma karbe ikon cibiyar kuma ya ja hankalin Amurka.

Kodayake Amurka tana ja da baya saboda rikicin Iraqi na yanzu ya shafi rikicin akida tsakanin mabiya Sunni da Shi’a. Amurka tana ganin gwamnatin Nuril Maliki ce ya kamata ta dauki matakan magance rikicin.

Sai dai kuma tura kwararru da Amurka zata yi a Iraqi na nufin zata taimakawa kasar kwato wasu biranen arewacin kasar da masu gwagwarmayar ‘Yan Sunni suka karbe, kafin su doshi Bagadaza.

Rikicin Iraqi dai yanzu jefa dubban mutanen kasar cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.