Maliki zai ɗauki mayaƙan sa-kai aikin Ƴan Sanda a Iraqi
Firaministan ƙasar Iraqi Nuri Al-maliki, ya yi alƙawarin samarwa mayaƙan sa-kai da ke mara masa baya a Lardin Anbar ta hanyar ɗaukar su aikin Ɗan sanda bayan sun murƙushe ma su yi wa gwamnatinsa bore. A kwanakin da suka gabata ne masu hamayya da gwamnatin Maliki, suka ƙwace ikon biranen fallujah da Ramadi da ke cikin lardin na Anbar, lamarin da ya yi sanadiyar ɓarkewar fada da kuma tserewar mutane sama da dubu uku daga yankin.
Wallafawa ranar:
Sai dai babu wani ƙayyadadden lokaci da gwamnatin Maliki tace zata aiwatar da alƙawalin na ɗaukar mayaƙan aikin Ƴan sanda inda tuni da yawansu suka rungumi makamai domin taimakawa Amurka yaƙi da Mayaƙan al Qaeda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu