Isa ga babban shafi
Pakistan

Sharif zai nemi sulhu da Taliban a Pakistan

Firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif yace zai nemi sasantawa da Kungiyar Taliban duk da jerin haren da kungiyar ta kaddamar a yankunan kasar. Amma Tuni Sharif ya nada kwamitin da zasu jagoranci tattaunawa da mayakan na Taliban.

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yana ganawa da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif shugabannin da ke fama da hare haren Taliban
Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yana ganawa da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif shugabannin da ke fama da hare haren Taliban REUTERS/S. Sabawoon/Pool
Talla

Mr Sharif ya shaidawa zauren Majalisar kasar cewa zai dauki matakin sulhuntawa da Taliban domin kawo karshen ta’addanci a Pakistan.

Kungiyar Taliban ta kaddamar da hare hare ne tun a bara da aka kashe shugabanta Hakimullah Mehsud a wani harin jiragen sama da Amurka ta kai a watan Nuwamba.

Mullah Fazlullah, wanda ya gaji Mehsud ya yi watsi da duk wani mataki na sulhu tare da shan alwashin daukar fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.