Isa ga babban shafi
Bangladesh

Jam’iyya mai mulki ta lashe zaben Bangladesh

Jam’iyyar Awami League mai mulki a Bangladesh ce ta lashe zabe gama-gari mai tattare da rikici da aka gudanar wanda ‘Yan adawa suka kauracewa. Yanzu haka Jam’iyyar ta yi watsi da kiran da kasashen duniya ke yi na ta shiga tattaunawa da ‘Yan adawa.

Magoya bayan Jam'iyyar BNP mai adawa a kasar Bangladesh
Magoya bayan Jam'iyyar BNP mai adawa a kasar Bangladesh Reuters
Talla

Kaurecewa zaben da ‘yan adawa suka yi, shi ne ya bai wa jama’iyya Awami League mai mulki nasara ba tare da hamayya ba.

An samu hasarar rayuka da dama a lokacin zaben. Inda aka ruwaito kashi 20 ne kacal na mutanen kasar suka fito kada kuri’a

Babbar Jam’iyar adawa ta Bangladesh Nationalist Party (BNP), da ta kauracewa zaben ta tsawaita yajin aikin da ta kira n agama-gari har zuwa ranar Laraba.

A lokacin zaben akwai dubun dubatar masu zanga zanga da suka cinna wa rumfunan zabe wuta a kasar.

Zuwa yanzu ‘yan sanda sun ce mutane 24 ne suka mutu, sai dai ‘yan adawan sun ce an kashe magoya bayansu a fito na fito da jami’an tsaro.

Tun kafin ranar zaben aka bayyana ‘yan takarar jama’iyya mai mulki da kawayenta, 153, a matsayin wadanda suka lashe zabe ba hamayya, daga cikin kujeru 300 na majalisar dokokin kasar.

Sakamakon farko da ya fito a takarar sauran kujeru 108 da aka yi, na nuna jama’iyyar ta Awami League mai mulki ta lashe mazabu 81, yayin da kawayenta, da ‘yan indefenda suka sami nasara a sauran 27.

Yanzu babbar damuwar gwammnati shi ne tashe tashen hankulan da ke nuna yadda kanun jama’a suka rabu, a kasar da ta balle daga Pakistan, bayan mummunan yakin da aka gwabza a shekarar 1971.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.