Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta zartas da hukuncin kisa ga wasu ‘yan tawaye Goma sha Shida 16.

Kasar Iran ta bayyana cewar ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane Goma sha Shida 16 bayan da aka yi kisan wasu mutane Goma sha Hudu 14 masu aikin gadin kan iyakar Kasar da Pakistan a wani yanki mai tsaunuka da Rikici ya barke.

Hukuncin kisa a Iran
Hukuncin kisa a Iran stop.torturing.us
Talla

An dai kaiwa wannan yankin mai tsaunuka na Sistan-Baluchestan na yankin kudu maso Gabashin Iran harin kwantar Bauna ne a cikin Samalainin Dare.

Wannan yankin dai an bayyana shi a matsayin mazaunin wasu ‘yan Sunni tsirarru Musulmi ba kamar sauran sassan kasar ba da mabiya akidar Shi’a suka mamaye.

An dai bayyana cewar akalla an kashe masu gadin kan Iyakar kasar Sha Hudu 14 a tashin hankalin daya faru a yankin na Sarayan, haka kuma wasu mutane Biyar 5 sun jikkata a wannan tashin hankali kamar yanda Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya bayyana a abinda ta kira daga kwakkwarar Majiya.

Wata majiya ta daban kuma ta bayyana maharan a matsayin masu son tada zaune tsaye a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, amma mataimakin Ministan harkokin cikin Gida na kasar Ali Abdollahi yace wasu fandararru ‘yan asalin kasar Iran ne suka kai wannan harin tare da kisan mutanen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.