Isa ga babban shafi
Philippine

An dakatar da binciken wadanda suka bata a hatsarin Jirgin Ruwan daukar kaya na Philipinu

Rahotanni daga kasar Philipinu, na nuna cewar adadin mutanen da suka bata a hadarin jirgin ruwan da ya auku a kasar Philipinu ya haura zuwa Tamanin da Takwas 85 daga mutane Dari da Saba’in da Daya 171 bayan an koma gudanar da wasu ayyukan ceto.

Aikin ceto a hatsarin Jirgin dakon Kaya na kasar Philipinu
Aikin ceto a hatsarin Jirgin dakon Kaya na kasar Philipinu REUTERS/Erik De Castro
Talla

A jiya Asabar ne matsanancin yanayi a kasar ya sa an jingine ayyukan neman mutane da suka bata bayan wani jirgin ruwan pasinja ya yi karo da wani jirgin kaya a kasar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane Talatin da Daya 31.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne hadarin ya auku ya yin da jirgin Pasinjan da ake kira St. Thomas Aquinas a Turance, da ke dauke da mutane sama da Dari Takwas 800 ya yi karo da wani jirgin kaya a cikin dare, lamarin da ya sa mutane sama da Dari Shida 600 suka nutse a cikin ruwa.

Mai magana da Yawun rundunar Sojin Ruwan kasar ta Philipinu Lieutenant Commander Gregory Fabic ya bayyanawa manema labarai cewar rashin kyakkyawan yanayi ne ya hana Direbobin Jirgin shiga kuryar Katafaren Jirgin da Ruwa suka mamaye, inda kuma ake sa Ran cewar akwai dimbin mutane a ciki da suka makale.

Sai dai ya bayyana cewar masu aikin ceto zasu yi iyakacin kokarin su, domin lalabo wadanda ke ciki, saboda sun san cewar akwai Salkar Iska a ciki kuma akwai yiyuwar samun wasu da Rayuwar su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.