Isa ga babban shafi
Qatar

Sarkin Qatar ya mika ragamar mulki ga Dan sa

Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa al Thani, ya mika ragamar tafi da kasar ga Dan sa, Sheikh Tamim bin Hamad al Thanim a wani sabon salon siyasa da aka samu a kasashen larabawa.

Sabon Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad al-Thani wanda ya gaji mahaifinsa Sheikh Hamad bin Khalifa al-Thani a ranar 25 ga watan Juni
Sabon Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad al-Thani wanda ya gaji mahaifinsa Sheikh Hamad bin Khalifa al-Thani a ranar 25 ga watan Juni REUTERS/Fadi Al-Assaad
Talla

Fadar Sarkin ta ware ranar Talata a matsayin ranar hutu ga al’ummar kasar bayan Sarkin da ya hambarar da mulkin mahaifinsa Sheikh Khalifa a watan Yunin shekarar 1995 kuma yanzu ya mika ragamar tafi da kasar ga na shi Dan.

Sabon Sarkin, Sheikh Hamad bin Khalifa al-Thani, mai shekaru 61, ya rike mukaman gwamnati a shekarun baya tare da taka rawa ga harakokin wajen Qatar musamman zanga-zangar da ta shafi sauran kasashen Larabawa.

A tsarin sarautar kasashen larabawa, wannan wani sabon salon siyasa ne domin kaucewa zanga-zangar da ta yi awon gaba da shugabannin kasashen Tunisia da Masar da Libya.

Gwamnatin kasar Qatar  tana sahun gaba cikin kasashen Larabawa da suka marawa ‘Yan tawayen Libya baya da kuma ‘Yan tawayen Syria da ke naman kawo karshen mulkin Bashar al Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.