Isa ga babban shafi
Syria

Kungiyar kasashe Larabawa ta yi kakkausar suka ga Israela kan hari a Siriya

Kungiyar tayi suka ne ga kasar Israela akan sake kai wa siriya tana bayyana hare-haren da cewar keta hurumin kasa-da-kasa ne. A nata haujin gwamnatin kasar Siriya ta bayyana cewa hare-haren da sojan saman Isra’ila suka kai a cikin kasar a jiya Assabar da kuma yau lahadi, da cewa wani ala’amari ne da ya bude kofar ‘’Komai na iya faruwa’’ duk da cewa kasar ba ta bayyana cewa ko za ta dauki fansa a kai ba.

Hari a kasar Siriya
Hari a kasar Siriya
Talla

Ministan yada labarai na kasar ta Syriya Omran Al-Zohbi, wanda ke gabatar da taron manema labarai a yau Assabar, ya bayyana hare-haren na Israela da cewa cin zarafi ne ga kasarsa ta Siriya.

Ita ma dai Kungiyar Kasashen Larabwa ta yi kakkausar suka game da harin da sojan saman Isra’ila suka kai a kan kasar Siriya inda kungiyar ta bukaci Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki wani mataki a kan Tel Aviv saboda ta keta dokokin kasa-da-kasa.

Wata sanarwa da ta fitar amadadin kungiyar ta kasashen Larabawa fadar shugaban kasar Masar ta bayyana harin da cewa ya sabawa ka’idojin kasa-da-kasa, kuma dole ne kasashen duniya su fito fili su bayyana rashin amincewarsu da shi.

Siriya dai ta kuma zargi Israela da taimakawa ‘yan tawayen kasar da Makamai kai tsaye domin yakar gwamnatin kasar, abinda ya keta ka’idar kasa-da-kasa na haramta safarar Makamai zuwa kasar ta Siriya.

Ida nana iya tunawa a ‘yan kwanakinnan ne kasashen Faransa da Burtaniya suka bukaci a basu damar kai makamai a Siriya domin yakar gwamnatin Bashar al-Assad, amma kungiyar tarayyar Turai tayi kashe cewar yin hakan zai kara tabarbara al’amurra ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.