Isa ga babban shafi
India

An kama mutumin da ke da hanu da yin garkuwa da wani jirgin India a shekarar 1999

Rundar ‘Yan sanda kasar India ta ce ta cafke wani mutum da ake zargi na da hanu a garkuwa da aka yi da wani jirgin fasinja a shekarar 1999. Mutumin wanda ake kira, Mehrajuddin Dand, an kamashi ne a Gundumar Kishtwar da ke Kashmir, bayan an share shekaru 13 ana farautar wadanda ke da hanu a lamarin.  

Firaministan India, Manmohan Singh
Firaministan India, Manmohan Singh Getty Images/Shekhar Yadav
Talla

Jirgin wanda a lokacin ke dauke da mutane 157 ya ke kuma kan hanyarsa ta zuwa birnin New Delhi an kwace shi ne a ka kuma kai shi garin Khandahar da ke kasar Afghanistan, jim kadan bayan jirgin ya tashi daga babban birnin Nepal, Kathmandu a ranar 24 ga watan Disambar shekarar 1999.

Ana dai zargin Dand da samarwa mutane biyar da su ka kwace jirgin laifin Fasfo a lokacin, inda ya yi ta hijra tsakanin iyakar India da Pakistan daga kuma karshe a samu aka kamashi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.