Isa ga babban shafi
Iran

Iran da kasashen Duniya sun koma teburin sasantawa

Iran da manyan kasashen Duniya sun sake komawa teburin sasantawa a birnin Moscow bayan an tashi baran-baram a tattaunawar farko tsakanin kasashen game da mallakar makamin Nukiliyar Iran.

Taron  manyan kasashen Duniya 6 tare da Iran game da Nukiliya
Taron manyan kasashen Duniya 6 tare da Iran game da Nukiliya REUTERS/Kirill Kudryavtsev/Pool
Talla

Kasar Amurka da Isra’ila sun ki yin watsi da kudirin daukar matakin Soji akan Iran da ke fuskantar jerin takunkumi saboda zargin mallakar makaman kare dangi.

Manyan kasashe Shida Masu shiga tsakanin rikicin sun bukaci Iran janye shirinta na inganta Uranuim da suke zargin wani tsari na samar da makamin nukiliya.

Tun kafin fara taron, manyan kasashen Duniya suna cike da tsammanin akan Iran zata iya canja manufarta, idan suka ci gaba da makala mata takunkumin sayar da man Fetir.

An gudanar da taron ne a wata Otel a birnin Moscow inda manyan kasashen guda shida suka yi hasashen Irankasar ta za ta ba da kai Bori yahau, amma kasar ta basu mamaki, ta hanyar yi wa bukatunsu kememe, harma tana cewar kasashen su dai na mafarkin zata jingine shirin makamashin Nukiliyarta domin tana yi ne don biyan bukatun kanta.

Manyan kasashen dai sun hada da Birtaniya da China da Faransa da Rasha da Amurka da Jamus.

An dade dai kasashen China da Rasha suna hawa kujerar Na-ki a zauren kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da kudirin daukar mataki akan Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.