Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Kasashen Duniya na Mayar da martani kan mutuwan Shugaban Koriya ta Arewa

Shugabanin Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani kan rasuwar shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-Il. Gwamnatin kasar China, wadda ita ce kawa kuma mafi kusanci ga shugaba Kim Jong-Il, ta bayyana kaduwar ta da rasuwar sa, inda nan take ta mika sakon ta’aziya, kuma ta bayyana tsohon shugaban a matsayin gwarzo, abokin tafiya.

Shugaban Koriya ta Arewa Marigayi Kim Jong il
Shugaban Koriya ta Arewa Marigayi Kim Jong il
Talla

China ta bayyana fatar ta, na ganin dangantakar kasashen biyu ta dore a bayan shugaba Kim.

Shugaban kasar Koriya ta kudu, Lee Myung Bak, ya bukaci 'yan kasarsa da su ci gaba da harkokin su kamar yadda suka saba, ba tare da wani tsoro ba, bayan tattaunawa da shugaba Barack Obama na Amurka ta waya, na sa’oi biyu, yayin da ya bukaci sojin kasar da su shiga cikin damara saboda kaucewa wata barazana.

Sakataren Gwamnatin Japan, Osamu Fujimura, ya bayyana fatarsu na ganin mutuwar bata haifar da tankiya a Yankin tekun Koriyan ba, inda ya ce an basu umurnin musayar bayanai tsakaninsu da Amurka, Koriya ta kudu, da China, da kuma shiga shirin ko ta kwana.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague, ya bayyana fatar kasarsa na ganin mutuwar ta bude wani sabon babi a siyasar kasar, da kuma hulda da sauran kasashen duniya, musamman akan shirin ta na samun makamin nukiliya, matsayin da ya yi daidai da na Ministan harkokin wajen Australia, Kevin Rudd.

Ita ma Amurka ta ce, tana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, kuma tana tattaunawa da kawayen ta, kamar yadda kakakin fadar shugaba Barack Obama, Jay Karney ya sanar.

Ministan harkokin wajen Sweden, Carl Bildt, ya ce mutuwar shugaban mulkin kama karya ko yaushe na haifar da fargaba a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.