Isa ga babban shafi
Isra'ila

Israila da Palestinu sabuwar takadama ta barke

Dakarun kasar Izraela sun buda wuta kan daruruwan Plastinawa da suka yi yunkuin kutsa kai a yankunan tuddan Golan da kasar Izraila ta mamaye tun cinkin 1967, inda suka kashe mutane 20 tare da jikkata wasu 277. A cewar gidan radiyon gwamnatin Israela, Palastinawa da dama ne aka kashe sakamakon tashin nakiyoyin da aka bibbine a yankin. Wanda harbin Bindiga ya tayar.Kafin faruwar hakan dai, wata murya da ta fito daga bututun magana na dakarun kasar ta Israela da suka taru gaban plastinawan domin tunawa da shekaru 44 da mamaye kasarsu da Izraelar ta yi, ta yi kashedin cewa duk wanda ya kuskura ya tsoma kafarsa a cikin yankin da aka killace to sunansa matace.Idan dai ba a manta ba ko a ranar 15 ga watan Mayun da ya gaba, a lokacin shagulgulan Nakba na tunawa da bakar ranar da aka kafa kasar Israela a gaban Idon Plastinawa, dubban Plastinawan ne suka yi yunkurin kutsa kai a cikin shamakin da Izraila ta shata inda nan take yenke dakarunta suka kashe plastinawa 13.Sake haduwar da plastinawa suka sake yi a jiya lahadi ta wakana ne sakamakon sanarwar da aka watsa ta shafin Facebook, inda suka dinga kada tutar kasar, tare da kokarin warware shigen wayar da Izrailar ta shata, sakamakon haka kuma dakarun na Israila suka buda wuta inda nan take suka kashe plastinawa 20 a yayin da wasu daruruwa suka jikkata.Amurika da wasu manyan kasashen duniya duk sun nuna takaicinsu dangane da faruwar lamarin, da dakarun na Israila suka aikata. 

Dutsin Golan
Dutsin Golan REUTERS/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.