Isa ga babban shafi
Japan

An Gano kimanin gawauwaki 2000 bayan girgizar kasa ta Japan

Gwamnatin kasar Japan ta bayyana cewa akwai yuwuwar narkewar sinadarin nukiya a biyu daga cikin tashoshin nukiyar da girgizar kasa ta Tsunami ta afkawa, yayin da masu aikin ceto suka gano kimanin gawauwaki 2000.Rohotanni daga kasar sun ce an samu wata fashewa a daya daga cikin tashoshin nukiliyar kasar ta Japan dake Fukushima.Hukumar dake kula da nukiliyar kasar, ta danganta fashewar da ci gaba da taruwar iskar hydrogen, amma jami’an gwamnati sun ce ba’a samu tsiyayar iska mai guba.Hukumar Kula da makamin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Japan ta sake sanar da dokar ta baci, a wuri na biyu da take da makaman nukiliya, sakamakon yoyon da aka samu.Masana Nukiliya a duniya sun bayyana cewa, duk da cewa har zuwa ba a samu wata fashewa mai karfi a cibiyar Nukliyar ta Fukushima, a kasar Japan ba, turirin sanadiran nukliyar da ke bin iska tun ranar Asabar da ta gabata na haifar da babbar barazana, wajen baza cututtuka a cikin jama’ar dake zaune a kewayen cibiyar.Yanzu haka dai tun bayan abkuwar girgizar kasar ranar Juma’a a kasar ta Japan, wace ta haifar da ambaliyar Tsunamin da ta shafi cibiyar samar da makamashin Nukliyar ta Fukushima, dubban daruruwan mutane ne dake zaune a kewayen cibiyar Nukiliyar da tazarar kilo mita 20, gwamnati ta kwashe sakamakon yadda lamura ke dada gurbacewa a yankin.Masana Nukilya sun ce, a halin yanzu jami’an ceto na kwana kwana dake aiki a yankin ne, ke cikin barazanar kamuwa da cututtukan da burbushin nukliyar ke haddasawa, inda suka ce yawan sanadarin nukliyar da a halin yanzu ke watayawa a cikin iska a yanki, zai iya haifar masu da cuta nan da makwanni ko watanni, ko ma nan da kwanaki 2 masu zuwa, cututukan da suka jibanci Hararwa. Ciwon gabban jiki, da kassansa,A lokacin wani taron manema labarai da ya kira a jiya PM kasar ta Japan Naoto Kan, ya bayyana cewa, kasar Japan ta fada a cikin mummunan hali, da bata taba samun kanta a ciki, tun bayan yakin duniya na biyu.

Wannan matar tana cikin wadanda girgizar kasa ta shafa
Wannan matar tana cikin wadanda girgizar kasa ta shafa REUTERS/Asahi Shimbun
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.