Isa ga babban shafi
Philippines

Wani Tsohon Dan Sanda yayi garkuwa da matafiya

WANI Tsohon Dan Sanda, dauke da makami, yayi garkuwa da wata motar safa, dake dauke da fasinjoji cikinsu harda Yan kasar Hong Kong 22.Kwamandan Yan Sandan birnin Manila, Leocadio Santiago, ya tabbatar da yara kanana a motar, kuma yace suna tattaunawa da wanda yayi garkuwar.Kwamandan ya bayyana wanda yayi garkuwar, a matsayin Rolando Mendoza, wanda aka kora daga aiki saboda zargin fashi da makami, tirsasawa mutane dan karbar kudi da kuma mu’amala da masu fataucin miyagun kwayoyi.Bayanan dake fitowa daga Manila, na nuan cewar, an saki yara kanana shida, tare dawani Dattijo, daga cikin wadanda ke cikin motar. 

Rolando Mendoza
Rolando Mendoza
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.