Isa ga babban shafi
Pakistan-Majalisar Dinkin Duniya

Ban ya sake kiran taimakon gaggawa ga Pakistan

SAKATARE Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bayyana kaduwar sa, da irin ta’adin day a ga ambaliyar ruwa ta yiwa kasar Pakistan, inda ya sake kiran baiwa kasar taimakon gaggawa.Bayan ziyarar yankunan da ambaliyar tayi ta’adi, tare da shugaba Asif Ali Zardari, Ban ya bayyana bala’in a matsayin abinda bai taba gani ba.Sakataren ya bukaci kasashen duniya, da kungiyoyin agaji, da su kai dauki wa kasar, musamman abinda ya shafi abinci, matsuguni da kuma magunguna.Ban yace, rashin daukar wanna mataki, na iya haifar da annobar da zata kaiga mummunar rasa rayuka, inda ya bayyana bada taimakon Dala miliyan 10, abinda ya kawo adadin Dala miliyan 27 da Majaisar Dinkin Duniya ta bayar yanzu haka.Gwamnatin kasar Pakistan tace, ambaliyar ta shafi mutane sama da miliyan 20.Shugaban kasar, Asif Ali Zardari, ya nemi fahimtar Yan Jaridu, da daukacin Yan kasar Pakistan, kan tafiyar da yayi zuwa kasashen waje lokacin barkewar ambaliyar, abinda ya janyo suka daga ko’ina.Zardari yace, irin bala’in da kasar ta fuskanta, ya fi karfin Gwamnatin kasar baki daya. 

SAKATARE Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon
SAKATARE Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon REUTERS/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.