Sudai kabilar gbage ko gwarawa a kan same sune galibi a jahohin Kaduna Niger; Nasarawa Niger da birnin tareyar Abuja, kuma a dukkan wadan nan jahohi kabilar gbage na da manyan sarkunan yanka masu daraja ta daya.Kabilar gbage dai an sansu ne da yin al-amuran su gwage gwage ta nan ne mallam Bahaushe ya lakaba mu su sunan gwari sunan da akafi sanin su da shi,ko da yake su yayan kabilar gwarin sun fiso ne a kira su da gbage;Haka kuma kabilarar gbagen na da wata al-adar da a fadin duniyar nan ba maiyin ta.wan nan alada dai an fisanin matan gwarawan ne da yinta.su dai matan gwarawa ba sa daukan duk wani abu a kan su, dan acewar su kai sarki ne.wanda ke dauke da kwakwalwa mai bawa dan adam tunani.Har gobe dai kabilar gbage na cigaba da gudanar da wan nan al-ada
Sauran kashi-kashi
-
Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.14/05/202410:02 -
Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.05/03/202410:02 -
Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.14/11/202310:19 -
Bafaranshiya ta lashe kyautar iya gasa biredi ta duniya
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta.31/10/202310:31 -
Shekaru 30 na Sarkin Masarautar Zazzau Suleja
Shirin Al'adunmu na wannan mako ya yada zango ne Masarautar Zazzau Suleja ta jihar Neja dake Najeriya domin shaida bikin murnar cika shekaru 30 na Sarkin Masarautar mai dimbin tarihi, Mallam Muhammadu Auwal Ibrahim, wanda ya kasance gwamnan jihar na farko na farar hula a jamhuriya ta biyu daga shekarar alif 979 zuwa alif 983.17/10/202310:00