Isa ga babban shafi

Morocco ta girbi kusan tan dari 3 na tabar wiwi a karon farko a hukumance

Morocco ta sanar girbe tabar wiwi tan 292 bayan da kasar ta arewacin Afrika ta halasta noman tabar a karon farko a shekarar 2023, wanda bayanai ke cewa kasar na son amfani da tabar don samar da magunguna da kuma amfanin masana’antu.

Kasashe da dama ssun fara halasta noman tabbar wiwi.
Kasashe da dama ssun fara halasta noman tabbar wiwi. AP - Richard Vogel
Talla

Hukuma ta musamman da Moroccon ta kafa don sanya idanu da kuma bibiyar yadda noman tabar ta wiwi zai gudana da ake kira ANRAC da kanta bayyana girbe tabar tan 294 wadda ta ce noman ya gudana bayan samun hadaka tsakanin bangarori 32 da ya kunshi manoma 430.

Babban jami’in hukumar ta ANRAC ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an gudanar da noman tabar ta wiwi a gonakin da ke da jumullar fadin kadada 277 da ke yankin arewacin kasar mai tsaunuka musamman garuruwan Al Houceima da Taounat da kuma Chefchaoueun.

A cewar ANRAC zuwa yanzu akwai akalla manoma 1500 wadanda suka raba kansu gida 130 da suka mika bukatar neman sahalewar gwamnati don gudanar da noman tabar ta wiwi a bana.

A shekarar 2023 ne Morocco ta halasta noman wiwi amma bisa tsauraran dokoki, matakin da sashen kula da magunguna na Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akwai bukatar sanya idanu matuka lura da yadda kasar a baya ke noman tabar ta haramtacciyar hanya a kadada dubu 47 cikin shekarar 2003 gabanin gwamnati ta yi sumame kan masu noman.

Morocco dai na matsayin kasa mafi noman tabar wiwi a arewacin Afrika inda galibin al’ummar kasar da ke rayuka a yankin arewaci mai tsaunuka suka dogara da nau’in noman wajen rayuwa.

Yanzu haka dai kasar ta arewacin Afrika ta samu lasisin fitar da tabar ta wiwi kasuwannin duniya akalla 54 daga bara zuwa bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.