Isa ga babban shafi

Cutar Lassa da ta barke a jihar Benue ta kashe mutane 13

Gwamnatin Banue da ke a arewa ta tsakiyar Najeriya ta bayyana cewa adadin mutanen da zazzabin Lassa ta kashe a kananan hukumonin jihar 9 da cutar ta barke a jihar ya kai 13 duk da kokarin da ta ke yi na dakile yaduwarta.

Hoto don misali
Hoto don misali © Daily Trust
Talla

A karshen makon da ya gabata, rahotanni sun ce mutum 9 ne cutar ta Lassa da bera ke yadawa ta kashe bayan barkewanta a wasu sassan jihar, yayin da daga bisani aka samu karin mutane 4 wadanda suka sa adadin ya haura zuwa 13.

Kwamishinan Lafiya na jihar Yanmar Ortese wanda ya bayyana hakan a yau Talata yayin taron manema labarai a birnin Makurdi fadar gwamnatin jihar, ya ce wayarwa al’umma kai kan cutar zai taimaka wurin gano wadanda ta kama tare magancewa akan lokaci.

Ya bayyana cewa, alkalumar Hukumar Lafiya ta Duniya ‘WHO’ ta bayyana Najeriya a matsayin kasar da ta fi yawan adadin masu kamuwa da cutar tare adadin wadanda suka mutu a duniya, biyo bayan yadda aka samu barkewar cutar sossai a shekarun da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.