Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Benin zata aikewa da Haiti taimakon sojoji dubu 2

Jamhuriyar Benin ta amince ta aike da sojoji dubu 2 zuwa Haiti a wani bangare na taimakawa kasar ta yankin Caribbean yaki da kungiyoyin ‘yan daba da suka addabi kasar.

Haiti ta dade tana fama da matsalolin 'yan daba da ke hallaka mutane ba ji ba gani
Haiti ta dade tana fama da matsalolin 'yan daba da ke hallaka mutane ba ji ba gani REUTERS/Charles Placide
Talla

Wakiliyar Amurka a majalisar dinkin duniya Linda Thomas-Greenfiled ce ta bayyana hakan, yayi wani taron manema labarai a birnin Guyana.

Sanarwar na zuwa ne dai-dai lokacin da Amurka ta ware dala miliyan 200 don taimakawa Haiti wajen samar da tsaro, abinda ke zama taimako mafi girma da wata kasa ta baiwa Haitin.

A watan Octoban bara ne dai majalisar dinkin duniya ta amincewa kasashe su baiwa Haitin tallafin sojoji a kokarinta na tabbatar da doka da oda a kasar.

Tun lokacin ne kuma kasashe musamman na Africa ke nuna sha’awar su ta taimakawa kasar.

Gwamnatin kenya wadda itace kasar Africa ta farko da ta nuna sha’awar ta na tura sojoji ta 1,000 zuwa kasar ta gamu da tutsun ‘yan majalisa dakuma kotu, sai dai duk da haka shugaba William Ruto ya sha alwashin ci gaba da shirin aikewa da sojojin ko da majalisar bata yarda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.