Isa ga babban shafi

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki a kasar, sakamakon tashin hankali da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa © Sawaba Radio
Talla

Yanzu haka Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, abinda ya tayar da zanga-zanga a wasu sassan kasar.

Wasu daga cikin ‘yan kasar sun jima suna kiraye-kirayen sojojin su kifar da gwamnatin Tinubu, matsawar abubuwa suka ki dai-daita.

To sai dai da take mayar da martani rundunar sojin kasar ta bakin daraktan tsaro Janar Christoper Musa ya ce masu wannan kiraye-kiraye basa nufin kasar da alkahairi, yayin da ya yi barzanar chafke masu wannan kiraye-kiraye.

Wannan ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar da dama
Wannan ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar da dama REUTERS/Akintunde Akinleye

 

Ya ce abinda sojoji zasu yi a yanzu shine kawai duba hanyoyin samar da sauki da kuma ciyar da kasar gaba, amma ba maganar juyin mulki ba.

Da yake amincewa da halin matsi da ‘yan Najeriya ke ciki, ganar Musa ya ce babu inda juyin mulki ke zama alkahairi a duniya don haka ba zasu yiwa Najeriya fatan ci bayan da yake biyo bayan juyin mulki ba.

Janar Musa ya bukaci ‘yan kasar da su kara hakuri da halin da ake ciki, sannan kuma su kasance masu juriya don cin moriyar tsare-tsaren da gwamnati ke bijirowa da su a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.