Isa ga babban shafi

Afirka na bukatar kara inganta shirin kawar da cutar HIV daga Amurka

Hukumar kula da lafiya ta Tarayyar Afirka ta ce  shugabannin nahiyar za su aike da sako na musaman ga kasar Amurka dun sabunta Shirin tallafin da take bayarwa wajen yaki da   rage yaduwar cutar kanjamau.

alamar wayar da kai game da cutar kanjamau
alamar wayar da kai game da cutar kanjamau AP - Ajit Solanki
Talla

Gwamnatin kasar Amurika ta kadamar da Shirin ne a shekarar 2003 da nufin bada tallafin gaggawa, da shawarwari da zumar ceton rayukan da cutar kanjamau ke kaiwa kabari, vayan samun goyon baya a majalisar dokokin Amurika.

Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka George W.Bush ya kaddamar, yana bayar da gudunmawar dalar Amurka biliyan 16 a duk shekara domin yaki da cutar HIV a Afirka.

Masu fafutukar kiwon lafiya sun damu da cewa rage tallafin yana jefa nasarorin da aka samu cikin haɗari.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce matakin rigakafin cutar kanjamau ya kai kashi 90 cikin 100 na adadin da ake bukata nan da shekarar 2025.

Ya zuwa shekarar 2022, akwai mutane miliyan 39 a duniya da ke dauke da cutar kanjamau, a cewar hukumar yaki da cutar AIDS ta Majalisar Dinkin Duniya. Daga cikinsu, miliyan 20.8 suna gabashi da kudancin Afirka.

Amma daga ciki sama da 9, ba su da damar samun magani na rage radadin cutar, Har da yara 600,000.

Majalisar dinkin Duniya ta fara bayyana kawo karshen cutar a 2015, amma  aka daga zuwa 2030, saboda wasu matsaloli da aka ci karo dasu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.