Isa ga babban shafi

Shugabar Hungary ta sauka daga mukaminta, sakamakon zarginta da goyon bayan masu fyade

Shugabar kasar Hungary Katalin Novak ta sanar da ajiye mukamin ta, sakamakon cecekucen da ya tashi a kasar bisa zargin ta da yafewa wasu mutane da kotu ta yankewa hukuncin zaman gidan yari a sakamakon kama su da laifin cin zarafin kananan yara.

Katalin Novak shugabar kasar Hungary
Katalin Novak shugabar kasar Hungary AP - Andrew Medichini
Talla

Wannan dambarwa dai ta samo asali ne bayan da shugabar ta yanke shawarar yafewa mataimakin shugaban wani gidan kula da kananan yara wanda ya taimaka wajen rufawa shugaban gidan asiri kan fyade da ya yiwa wasu kananan yara.

Jim kadan bayan wannan sanarwa tata, kuma sai ministar shari’a ta kasar Judit Varga itama ta sanar da janyewar ta daga duk wata harka ta siyasa da aikin gwamnati, duk dai kan wannan batu.

‘Yan adawa dai sune suka rura wutar wannan cecekuce da ke alakanta shugabar kasar da goyon bayan masu cin zarafin kanan yara a fakaice.

A wata takarda ta ta mikawa prime ministan kasar Victor Orban, shugaba Novak, mai shekaru 46 ta ce zata bar aiki a sakamakon fushin da ‘yan kasar ke yi da ita kan matakin da ta dauka wanda a ganin ta shine dai-dai.

Takardar ta kuma kunshi ban hakuri da neman yafiya a gurin wadanda matakin nata ya fusata, tana mai cewa ta yanfe musu ne ba don tana goyon bayan laifin da suka aikata ba.

Novak wadda tsohuwar minister kula da harkokin iyali ce, ta ce ta san daraja da kuma kimar da kananan yara ke da shi, kuma ta bada gudumowa kwarai wajen ganin sun samu kariya a dokokin kasar.

Novak dai itace mace ta farko da ta fara rike wannan mukami, wanda ta fara tun 2022.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.