Isa ga babban shafi

Amurka ta caccaki Senegal saboda jinkirta zaben kasar

Amurka ta soki yadda shugaban kasar Senegal ya jinkirta zaben kasar tare da kama wasu ‘yan majalisar dokokin bayan wata muhawara mai zafi da suka gwabza a majalisar yayin zaman duba lamarin halin da da kasar ta shiga.

Shugaban Senegal Mack Sall
Shugaban Senegal Mack Sall © AP/Christophe Ena
Talla

 

Amurka ta bayyana matsayin nata ne bayan da shugaban na Senegal ya daga zaben da aka shirya yi a wannan wata da muke ciki, tare bukatar ganin kasar ta mutunta kundin tsarin mulkinta.  

 

Haramta matakin na Senegal ya biyo bayan yadda ‘yan sandan kasar suka dauki matakin ba sani ba sabo wajen dakile duk wanda ya yi adawa da  shugaba Macky Sall na jinkirta zaben da aka shirya gudanarwa a cikin wannan wata.

A ranar 5 ga watan Fabrairun nan ne ‘yan sandan suka daka wa masu zanga zangar adawa da shirin na shugaban kasar a gaban zauren majalisar kan dakatar da zaben wawa tare da kama wasu da dama.

 

A ranar Litinin da ta gabata ne majalisar dokokin kasar ta amince da batun dage zaben da shugaba Macky Sall ya yi bayan wata muhawara da yi a zamansu na ranar.

 

Har ila yau a wannan rana wasu ‘yan majalisar su biyu suka gabatar da kara domin kalubalantar hukuncin shugaban kasar na jinkirta zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 25  ga watan Fabrairun da muke ciki.

 

Sai dai Kungiyar Kasashen Afirka ta AU ta bukaci gwamnatin Senegal da ta gaggauta shirya zabe tare kira ga ‘yan takarar da su yi abin da ya dace wajen samun fahimtar juna ta hanyar tuntubar juna da tattauna lamuran da za su samar da mikakkiyar hanyar gudanar da zabe ba tare samun wata matsala ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.