Najeriya, DR Congo, Afrika ta Kudu da Cote D’Ivoire sun kai matakin kusa da karshe
A gasar cin kofin Afrika,kungiyar Cote D’Ivoire mai masaukin baki ta lallasa kasar Mali da ci 2 da 1, yayinda Afrika ta Kudu ta doke Cap Vert ,nasarar da ke baiwa kungiyar damar tsallakawa matakin daf da na karshe a wannan gasa.
Wallafawa ranar:
Yanzu kam kungiyoyi hudu ne suka rage a wannan tafiya,kuma daya daga cikin wadanan kungiyoyi da suka hada da Najeriya,Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo,Afrika ta Kudu da Cote D’Ivoire mai masaukin baki ne za ta dage wannan kofi.
A bangaren Najeriya,wannan kungiya ta taba haduwa da Afrika ta kudu lokacin yan wasa irin su Jay Jay Okocha a shekara ta 2000 a wannan mataki na wasan daf da na karshe,wanda Najeriya ta yi nasara da ci 2 da nema kafin daga bisani Kamaru ta doke ta a wasan karshe.
Haka zalika Cote D’Ivoire ta taba haduwa da wannan kungiya a 2015 a wannan mataki karkashin jagorancin mai horarwa Herve Renard,inda Cote D’Ivoire ta lallasa DRCongo da ci 3 da 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu