Isa ga babban shafi

Dakarun MINUSMA a Mali sun mika sansaninsu na Tumbuktu ga sojojin kasar

Dakarun wanzar da zaman lafiya na malisar dinkin duniya MINUSMA sun mikawa gwamnatin sojin Mali guda daga cikin manyan sansaninsu da ke yankin Tumbuktu na arewacin kasar, abinda ke zuwa kafin karkare ficewar su daga kasar baki daya.

Taswirar kasar Mali
Taswirar kasar Mali © Studio graphique FMM
Talla

Dama sansanin Gao da na Tumbuktu sune sansanoni na karshe da sojojin na MINUSMA basu kai ga mika su ga jamia’n sojojin kasar a hukumance ba, kasancewar daya ga watan sabuwar shekara ne zai cika wa’adin da aka debar musu na ficewa daga kasar.

Bayanai sunce bayan sansanin dakarun na MINUSMA sun kuma hannantawa gwamnatin sojin wasu kayayakin aiki da makamai.

To sai dai wani abin fargaba shine yadda hare-haren kungiyoyin masu ikirarin jihadi ke kara zafafa, dai-dai lokacin da sojojin ke tattara nasu ya nasu, abinda ke jefa shakkun cewa anya sojojin na Mali zasu iya magance matsalar su kadai kuwa?

Wata majiyar majalisar dinkin duniya da ta bukaci kamfanin dillanci labaran Faransa AFP ya sakaya ta, ta ce a yanzu majalisar dinkin duniya bata da wani zabi illa ta fice daga kasar, saboda yadda aka gaza cimma dai-daito tsakanin ta da sojojin kasar.

Motocin dakarun MINUSMA a Mali
Motocin dakarun MINUSMA a Mali AFP/Archivos

Majiyar ta kuma kara da cewa babban abin tashin hankalin shine yadda alamu ke nuna cewa masu ikirarin zasu ci gaba da kwace garuruwan da kisan jama’ar da basu ji ba basu gani ba.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin dakarun na MINUSMA da ke aiki a kasar da sojojin Mali tun bayan juyin mulkin 2020 lamarin da ya tilasta wa dakarun ficewa daga kasar ba don suna so ba.

Kididdiga ta nuna cewa majalisar dinkin duniya tana da sojoji sama da dubu 15 a Mali wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.