Isa ga babban shafi

Garin da ake samun walwala a Sudan ya shiga rudani

Sojojin Sudan sun hana fararen hula shiga birnin Wad Madani a yau Juma’a, yayin da wani dan jaridar AFP ya hangi jiragen yaki na shawagi a sararin samniyar garin, inda kuma ake ta jin karar fashewar abubuwa a cikinsa.

Mutane na hada-hada a garin Wad Madani, na Sudan
Mutane na hada-hada a garin Wad Madani, na Sudan AFP - -
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga wata na tara na fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai na RSF da ke kasar ta Sudan.

Tun lokacin da yakin ya barke a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata, garin na Wad-Madani mai tazarar kilomita 180 daga kudancin birnin Kharthoum, ya zama tudun-mun-tsita ga jama’ar da ke guje wa rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, garin na Wad-Madani na dauke mutane rabin miliyan da ke samun mafaka a cikinsa bayan sun rasa muhallansu.

Da farko dai, yakin na Sudan bai shiga cikin wannan garin ba, amma a watannin baya-bayan nan, an ga yadda mayakan suka rika dirar wa garin sannu a hankali, inda suka yi ta tattaro dakaru suna kuma kafa shingayen binciken ababen hawa tsakanin garin da birnin Khartoum

Masu amfani da shafukan sada zumunta da ke garin sun yi ta yada wasu hotuna da ke nuna yadda hayaki ke turnuke sararin samaniyar garin, yayin da suke cikin fargabar yiwuwar sake neman wani tudun-mun-tsiran na daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.