Isa ga babban shafi

Kayan abinci sun kare a sansanin 'yan gudun hijirar Sudan da ke Chadi - MDD

Hukumar samar da abinci ta duniya ya ce tallafin abinci da aka tarawa 'yan gudun hijira sama da rabin miliyan da suka tsere daga Sudan zuwa Chadi na daf da karewa.

Wasu mata 'yan gudun hijira kenan, da suka tserewa rikicin Sudan zuwa kasar Chadi.
Amne Moustapha, une réfugiée soudanaise enceinte qui a fui la violence dans son pays, avec d'autres réfugiés près de la frontière entre le Soudan et le Tchad, à Koufroun, le 28 avril, 2023. REUTERS - MAHAMAT RAMADANE
Talla

Daraktan hukumar a kasar Chadi, Pierre Hnnorat, ya shaidawa Reuters cewa, nan da watan Disamba, duk wani tallafin abinci da ake bawa ‘yan gudun hijirar zai kare, don haka suna neman daukin gaggawa.

Sama da ‘yan gudun hijira 540,000 ne suka tsere daga Sudan zuwa Chad, tun vayan rikicin da ya balle watanni bakwai da suka gabata, tsakanin dakarun gwamnati da kuma dakarun kai daukin gaggawa na RSF, a cewar hukumar kula da kaurar jama’a ta duniya.

Wadanda suka shiga kasar a bana, tuni suka yada zango a sansanin ‘yan gudun hijirar da aka samar a Chadi, inda Honnorat ya ce rayuwa tana musu wahala saboda bukatar taimakon jin kai.

Ya ce, suna bukatar akalla dala miliyan 25 a kowanne wata, domin ciyar da yan gudun hijira sama da 800,000.

Rikicin Sudan ya taimaka wajen haifar da tsananin yunwa, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ta raba tsabar abincin da zai ciyar da mutane miliyan 13 zuwa miliyan 19, vayan da yakin kasar ya haifar da cikas ga sha’anin noma.

A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya, sama da mutum miliyan 20 daga cikin miliyan 49 na fama da matsananciyar yunwa yanzzu haka, inda ta bukaci daukar matakan gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.