Isa ga babban shafi

Ana fargabar karancin abinci a sansanin 'yan gudun hijirar Sudan

Majalisar Dinkin duniya ta yi gargadin cewa bayanan da ta samu na nuni da yiwuwar fuskantar karancin abinci a sansanonin ‘yan Sudan dake zaman gudun hijira a Chadi.  

Біженці із Західного Дарфуру у Чаді, липень 2023
Wasu 'yan gudun hijirar Sudan © Zohra Bensembra / Reuters
Talla

 

Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ce ta bayyana wannan fargaba a yayin da ta ce ‘yan gudun hijira sama da dubu 500 da suka shiga Chadi daga Sudan na iya fuskantar karancin abinci saboda karancin isassun kudaden gudanar da laumura. 

Sai dai shugaban hukumar ta Majailsar Dinkin Duniya Pierre Honnorat ya bayyana cewa ya kamata a gaggauta samar da kudaden ci gaba da gudanar da ayyukan samar da abincin don kiyaye fuskantar halin kaka-nika-yi a tsakanin ‘yan gudun hijirar. 

Hukumar Kula da Kaurar Jama’a ta Duniya ta bayyana cewa ‘yan gudun hijira sama da dubu 540 ne suka ketare zuwa Sudan  tun bayan barkewar rikici a tsakanin sojojin Sudan da dakarun daukin gaggawa na RSF watanni bakawai da suka gabata. 

Daga farkon yakin, fararen hula da dama ne suka tsere daga birnin El-Geneina da ke yammacin Darfur yankin da rikicin kabilanci ya  daidaita. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.