Isa ga babban shafi
Rikicin Sudan

An kashe mutane 700 cikin kwana biyu a Sudan

Hukumar Kula da Kaurar Baki ta Duniya ta bayyana cewa, kimanin mutane 700 aka kashe a Yammacin Dafur a wani fada da aka gwabza tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai na RSF a cikin wannan wata na Nuwamba.

Hayaki ya turnuke sararin samaniya a Sudan
Hayaki ya turnuke sararin samaniya a Sudan REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Sanarwar da Hukumar Kula da Kaurar Bakin ta Duniya ta fitar ta ce, an gwabza wannan fadan ne a ranakun 4 da 5 ga watan da muke ciki na Nuwamba a birnin El Geneina.

Sanarwar ta ce, akwai kuma karin mutane 100 da suka samu rauni, yayin da wasu 300 suka yi batan-dabo babu labarinsu har yanzu.

A bangare guda,  wasu bayanai na daban da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na cewa, an samu asarar rayukan mutane sama da 800 duk dai a yankin na Dafur sakamakon artabun da aka yi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai.

Dakarun RSF da ke yaki da gwamnatin Sudan.
Dakarun RSF da ke yaki da gwamnatin Sudan. AFP - -

Akwai kuma gidaje har guda 100 da jama’a ke samun mafaka da su ma aka kona su kurmus, yayin da wasu bata-gari ke amfani da wannan dama wajen sace-sacen dukiyoyin al’lumma da suka hada da  kayayyakin jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya.

Yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da ta’azzarar matsalolin take hakkin bil’adama a Yammacin  Dafur a daidai lokacin da rikicin watanni bakwai ya yi kamari a Sudan.

Shekaru 20 da suka gabata, duniya ta kadu da abin da ya faru na take hakkin bil’adama a Dafur, abin da ya sa ake fargabar aukuwar makamancin wancan al’amari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.