Isa ga babban shafi

Shekaru 10 da yi wa 'yan jaridar RFI kisan gilla a Mali

Yau ake cika shekaru 10 da kisan gillar da ‘yan ta’adda suka yiwa ‘yan jaridun RFI Ghislane Dupont da Claude Verlon a kasar Mali, amma har ya zuwa wannan lokaci ana ci gaba da tababa akan dalilin hallaka ma’aikatan yada labaran. 

'Yan Jaridar Radio France International  da aka kashe a Kidal na kasar Mali Claude Verlon da Ghislaine Dupont a ranar 2/11/2013.
'Yan Jaridar Radio France International da aka kashe a Kidal na kasar Mali Claude Verlon da Ghislaine Dupont a ranar 2/11/2013. RFI
Talla

A ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2013 ne akayi garkuwa da Ghislane Dupont da mataimaka mata Claude Verlon tare da hallaka su lokacin da suke gudanar da aiki a Kidal, kamar yadda FMM da ta mallaki RFI ta sanar. 

Sanarwar ta ce har ya zuwa wannan lokaci babu wani gamsashen bayani a kan dalilin kama su da kuma hallaka su, yayin da iyalansu ke fargabar cewar ba za a iya hukunta wadanda suka aikata laifin ba, ganin cewar sauran mutum guda ne ke da rai daga cikin ‘yan bindigar da suka hallaka su. 

An dai gano mutane 4 daga cikin mayakan da suka aikata kisan gillar, kuma RFI ta gabatar da kara a kai tare da ci gaba da bin shari’ar. 

‘Yar uwar Verlon, Marie-Pierre Ritleng ta bayyana cewar ana ci gaba da bincike akai, amma kuma yana tafiyar hawainiya, yayin da ta bayyana fargabar cewar zai dauki dogon lokaci kafin samo amsa dangane da abinda ya sa suka aikata kisan. 

Ita kuwa mahaifiyar Dupont, Marie-Solange Poinsot ta shaidawa RFI cewar har yanzu ta na zub da hawaye kowacce rana a kan kisan da aka yiwa ‘diyarta. 

‘Ina matukar juyayin rabuwa da ita sosai, saboda itace farin cikin rayuwa ta’, yayin da take bayyana cewar watakila sai bayan ranta a aiwatar da hukunci a kan kisan. 

Poinsot mai shekaru 93 ta bayyana cewar akwai alamun sojojin Faransa na boye wasu muhimman bayanai dangane da kisan, watakila domin kare kansu. 

Wata majiya daga hukumomin Faransa sun ce akwai sojojin kasar da dama a Kidal a ranar da aka hallaka ma’aikatan guda biyu, amma basu da isassun kayan aikin da zasu kare lafiyar su. 

Wasu rahotanni farko sun ce akwai tazarar akalla mintina 20 tsakanin lokacin da akayi shelar garkuwa da ‘yan jaridun da kuma lokacin da zaratan sojojin Faransar suka kai dauki. 

‘Yar Verlon, Apolline ta rubuta wasika ga shugaba Emmanuel Macron da uwargidansa Brigitte Macron domin bayyana labaran gaskiya ga iyalan ma’aikatan dangane da abinda ya faru. 

A wannan shekarar, ta shaidawa RFI cewar tana bukatar sanin gaskiyar lamarin domin ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali tare da kauda shakku game da abinda ya faru a wannan ranar ta 2 ga watan Nuwambar shekarar 2013. 

Sakamakon bukatar da RFI ta gabatar, Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 2 ga watan Nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar yaki domin kawo karshen cin zarafin ‘yan jaridu ta duniya. 

RFI ta amince ta karrama Dupont da Verlon ta hanyar horar da matasa ‘yan jaridu daga kasashen Afirka, yayin da aka gudanar da biki na musamman a Abidjan ta kasar Cote d’Ivoire domin karrama wadanda suka ci gajiyar horon. 

An kirkiro guraban karo ilimin Ghislaine Dupont da Claude Verlon ne domin karrama ‘yan jaridun guda biyu, kamar yadda sanarwar FMM ta bayyana, domin yada ilimi da manufarsu ga ‘yan jaridu da ma’aikatan yada labarai, wadanda suka yi aiki tare da su a tashar RFI ko kuma a filin dauko rahotanni. 

Ku latsa alamar sauti don jin rahoton da Abdoulaye Issa ya hada kai...

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.