Isa ga babban shafi

A Kinshasa, Mélenchon ya ba da lambar yabo ga jarumin 'yancin kai Lumumba

Jean Luc Melenchon, shugaban masu tsattsauran ra'ayi na Faransa a wata ziyara da yak ai DRCongo ya yi kira a jiya Asabar a Kinshasa  da a yi tuni da jarumi kuma dan kishin Africa Patrice Lumumba .

Jean Luc Melenchon dan siyasar Faransa
Jean Luc Melenchon dan siyasar Faransa AFP - BERTRAND GUAY
Talla

Tsohon dan takarar shugaban kasar Faransa, Jean Luc Mélenchon ya isa DRCongo, a wannan ziyara na tsawon mako guda, tare da rakiyar tawagar mataimakansa uku daga jam’iyyar sa, La France Insoumise.

Shugaban kasar Félix Tshisekedi ya karbe shi a ranar Alhamis, Melenchon ya ba da goyon baya mai karfi ga hukumomin DRC a kan Rwanda, wanda ya yi Allah wadai da  goyon bayan da Rwanda ke baiwa yan Tawayen  M23  a gabashin Congo.

Patrice Lumumba a shekar  1960.
Patrice Lumumba a shekar 1960. © AFP

"Muna fuskantar kisan kiyashi da yawa, da ban tsoro da yawa, da abubuwan banƙyama masu yawa, tare da kowane ɓangarorin a cewar Jean Luc Melenchon.

Jean Luc Melenchon Dan siyasar Faransa
Jean Luc Melenchon Dan siyasar Faransa © AP - Michel Euler

A wani kokari na tuni da tarihi ,Melenchon ya duba tarihi da cewa : ranar 17 ga watan Junairun shekarar 1961 ne 'yan awaren Katanga da sojojin hayar Belgium suka kashe Patrice Lumumba Firaministan kasar mai cin gashin kanta. Dan siyasar ya bayyana takaincin sa kai, a karshe ya girmama Patrice Lumumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.