Isa ga babban shafi

Daliban Nijar da Mali da Burkina Faso sun shiga rudani saboda bisar Faransa

Daruruwan dalibai da masu bincike da masu fasahar zane-zane da ke burin balaguro zuwa Faransa sun shiga dimuwa sakamakon fargabar rashin samun takardun bisa saboda yadda kasashensu na Burkina Faso da Mali da Nijar suka shiga takun-saka da Faransa biyo bayan juyin mulkin soji.

Wasu daliban Afrika
Wasu daliban Afrika AP - Jerome Delay
Talla

Sojojin da suka yi juyin mulki a wadannan kasashen sun shiga takaddama da uwargijiyarsu Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka, inda har suka kori sojojinta da jakadunta.

Masu cacccakar Faransa sun bayyana ta a matsayin wadda ke son yin babakere wajen tafiyar da tattalin arziki da siyasar wadannan kasashe na Afrika, zargin da gwamnatin Paris ta sha musantawa.

Yanzu haka Faransa ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke Burkina Faso da Mali da Nijar saboda fargabar rashin tsaro a daidai lokacin da kasashen suka juya mata baya tun bayan da sojoji suka kwace mulki daga hannun farar hula.

Takaddamar bayar da bisa da kuma dakatar da tallafin Faransa ga kasashen uku na zuwa ne a yayin da shugaba Emmanuel Macron ke naman sake kulla alaka da kasashen a daidai lokacin da Rasha da China ke rige-rigen samun karbuwa a nahiyar Afrika.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da wasu dalibai
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da wasu dalibai AP - Ludovic Marin

A bara kadai, Faransa ta bai wa dalibai daga Burkina Faso har su 907 takardun bisa, kamar yadda ta bai wa 'yan asalin Mali 689 takardun na bisa, inda ta bai wa 'yan Nijar 436 bisar da ke son karatun wucen-gadi a kasar kamar yadda wata majiyar diflomasiya ta  bayyana.

Sai dai a wannan shekarar, dalibai da likitoci da masu fasahar zane-zane har ma da 'yan kasuwa daga kasashen uku na yankin Sahel na ci gaba da nazari kan yadda za su shawo kan wannan matsalar ta rashin samun takardun bisa don komawarsu Faransa, kasar da suka shafe gomman shekaru a cikinta suna gudanar da harkokinsu.

Kodayake mahukuntan Faransa sun bayyana cewa, daliban kasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar da yanzu haka ke zaune a Faransar, za su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fuskantar wata tsangwama ba.

Akwai sama da dalibai dubu 3 da 100 daga Mali da kuma dubu 2 da 300 daga Burkina Faso, sai kuma dubu 1 da 100 daga Nijar da dukkaninsu ke karatu a makarantun Faransa kamar yadda wasu alkaluman da Hukumar Kula da Manyan Makarantu daga Ketare ta kasar ta fitar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.