Isa ga babban shafi

Ba zamu zuba ido ayi amfani da karfin Soji kan Nijar ba - Mali

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya yi gargadin cewa kasar ba za ta zuba ido ba tare da daukar mataki ba, idan har ECOWAS da wasu kasashen duniya suka yi yunkurin amfani da karfin Soji kan Jamhuriyar Nijar, bayan juyin mulkin da Sojoji suka yi.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop yayin jawabi gaban taron Majalisar Dinkin Duniya.
Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop yayin jawabi gaban taron Majalisar Dinkin Duniya. © United Nations
Talla

A jawabin da ya gabatar gaban zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, babban jami’in diflomasiyyar na Mali ya ce lura da yarjejeniyar tsaron da ke tsakaninsu da Nijar, dole ne su kai mata dauki da zarar aka yi yunkurin afka mata.

A makon da ta gabata ne, kasashen Mali da Nijar da Burkian Faso suka kulla wata yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu don taimakekeniyar juna, lura da yadda dukkaninsu ke karkashin mulkin Soji.

Nijar ce kasa ta baya-baya a yankin yammacin Afrika da ta fuskanci juyin mulki bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin halastaccen shugaba Bazoum Mohamed a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Cikin jawabin na sa Abdoulaye Diop ya yi kakkausar suka ga yunkurin amfani da karfin Soji kan Nijar ya na mai cewa Mali ba za ta aminta da duk wani shirin ECOWAS na amfani da karfin Soji kan makwabciyar ta su ba.

A cewarsa duk wani yunkurin shigar sojin ketare don yakar jagorancin wata kasa kai tsaya barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar al’ummarta dama yankin yammacin Afrika baki daya wanda kuma baza su zuba ido hakan ya faru ba.

Cikin jawabin nasa ministan harkokin wajen na Rasha ya kuma yaba da kokarin Rasha wajen tallafawa kasashen yankin Sahel a yakin da suke da matsalolin tsaron da suka dabaibayesu baya ga kakkausar suka ga Faransa da kawayenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.