Isa ga babban shafi

'Yan ta da kayar baya a DR Congo sun ratayawa wasu tagwayen jira-jirai bam

Wasu 'Yan ta da kayar baya a Jamhuriyar dimokaradiyar Congo sun rataya wa wasu jira-jirai tagwaye kuma mata jigidar bam a yunkurin su na kaiwa sojoji hari.

Goma, daya daga cikin yankunan dake fama da rikici a DR Congo
Goma, daya daga cikin yankunan dake fama da rikici a DR Congo AFP/Junior D. Kannah
Talla

‘Yan ta da kayar bayan sun daura jigidar ababen fashewa a jikin  wasu tagwayen jarirari mata da zummar kai hari kan wasu dakarun tsaron kasar, wanda majalisar dinkin duniya ta bayyanma a matsayin cin zarafin kananan yara.

Hukumar kula da kananan yara ta UNICEF ta ce an gano ‘yan matan biyu ‘yan shekara daya ne a wani kauye da ke arewacin Kivu, yankin da kungiyar ‘yan bindiga da aka fi sani da Allied Democratic Forces ADF da kara kaimi wajen kai hare-haren bama-bamai.

masana ne a fannin kwance bama-bamai suka kwance Bam din ba tare da ya tashi ba, abinda ya sa aka samu nasarar ceto jira-jiran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.