Isa ga babban shafi

Ba don Faransa ba da wasu kasashen Afrika sun rushe - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sake jadadda muhimmancin da kasar ke da shi ga tsaron yankin Sahel, yana mai cewa ba don kokarin da sojojin Faransa ke yi ba, da yanzu wasu kasashen Afrika sun rushe. 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron via REUTERS - POOL
Talla

 

Wannan na zuwa ne bayan da kasashe rainon Faransa musamman na yankin Sahel ke ci gaba da kufcewa daga hannun ‘yan dimkoradiyya, yayin da adawa da kasancewar Faransa a wadannan kasashe ke kara kamari. 

A wata tattaunawa da manema labarai, shugaba Macron ya ce ba za a tabbatar da irin kokarin da sojojinsa ke yi a irin wadannan kasashe ba, har sai an hango yadda za su kasance idan babu sanya hannun Faransa a tabbatar da tsaron. 

A shekarar da ta gabata Faransa ta kara yawan sojojinta da ke rundunar Barkhane mai yaki da ta’addanci zuwa dubu 5,100, sai dai kuma jama’a da gwamnatin sojin wadannan kasashe na korafin cewa, hakan ba shi da wani tasiri. 

Shugaba Macron ya kuma bigi kirjin cewa, nasarar da suka samu ta fannin tsaro a kasashen ta zarta wadda wasu kasashen duniya da Kungiyar Tarayyar Turai suka samu idan an hada waje guda, yana mai cewa nan ba da jimawa za su sake sabon salon tunkarar ‘yan ta’addar a irin wadannan kasashe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.