Isa ga babban shafi

Yajin aikin masu motocin haya ya rikide zuwa tashin hankali a Afirka ta Kudu

An kashe mutane biyar a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, bayan da yajin aikin da direbobin motocin haya ke yi rikide zuwa tashin hankali.

Wasu mazauna yankin Masiphumelele bayan kafa shinge tare da, yayin yajin aikin da masu motocin haya ke ci gaba da yi a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, 8 ga Agusta, 2023
Wasu mazauna yankin Masiphumelele bayan kafa shinge tare da, yayin yajin aikin da masu motocin haya ke ci gaba da yi a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, 8 ga Agusta, 2023 © Nic Bothma / Reuters
Talla

Tun a makon jiya direbobin motocin hayar suka fara yajin aiki domin adawa da wata sabuwar doka da ta bai wa mahukuntan karamar hukumar ikon kama ababen hawa, muddin aka samu direbobinsu da laifukan da suka hada da tuki ba tare da lasisi ba, ko kuma amfani da motoci marasa lamba.

A ranar Alhamis da ta gabata, kungiyar masu motocin haya ta Afirka ta Kudu mai suna ‘SANTACO’, ta sanar da shiga yajin aikin dakatar da sufuri na tsawon mako guda, bayan da ta gaza warware rashin jituwar da ke tsakaninta da gwamnatin yankin karamar hukumar Cape Town.  

Bayanai sun ce an fuskanci barkewar rikici a sassan birnin, bayan 'yan sanda suka fara kama motoci a makon da ya gabata, abinda ya fusata masu zanga-zanga da wasunsu suka kona motoci manya da kanana, tare da yi wa 'yan sanda rotse da duwatsu.

Rundunar ‘yan sandan Afira ta Kudu ta ce ya zuwa yanzu mutane 120 jami’an tsaro suka cafke a bisa zarginsu lalata dukiya, da kuma kuntuka sata da sunan kwasar ganima, baya ga tayar da hankalin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.