Isa ga babban shafi

OPEC ta yi kakkausar suka ga kiraye-kirayen hana kasashen Afrika hakar fetur da gas

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta yi kakkausar suka ga kiraye-kirayen da ake yi wa kasashen Afrika na daina zuba kudade wajen hako albarkatun man fetur da iskar wanda kungiyoyin kare muhalli ke ganin ya na taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhalli.

Masu fafutukar muhalli na alakanta gurbacewar yanayi da hakar makamashin da kasashe ke yi.
Masu fafutukar muhalli na alakanta gurbacewar yanayi da hakar makamashin da kasashe ke yi. AFP/File
Talla

Babban sakataren kungiyar ta OPEC Haitham Ghais yayin jawabinsa gaban taron bunkasa makomar bangaren makamashi na Najeriya karo na 22 ya  bayyana cewa kiraye-kirayen dakatar zuba jarin hakar makamashin a Afrika tamkar bita da kulli ne, lura da yadda nahiyar baki daya ke taimakawa da kasa da kasha 3 kacal na tiririn da ke gurbata muhalli.

A cewar Ghais wannan kiraye-kiraye tamkar manakisa ce ga yunkurin kasashen Afrikan na gina kawunansu ta hanyar kudaden da suke samu a bangaren makamashi kuma har zuwa yanzu basu kai matakin da za su iya illa ga gurbacewar muhalli ba.

Babban sakataren kungiyar ta OPEC ya bayyana cewa yanzu haka kasashen masu arzikin man fetur na bukatar zuba jarin dala tiriliyan 12 daga yanzu zuwa shekarar 2045 don habaka tattalin arzikinsu da kuma samar da ayyukan more rayuwa, yayinda wannan kiraye-kiraye ke matsayin karantsaye ga bukatunsu.

 A cewar sakataren na OPEC wannan kiraye-kiraye daga kungiyoyin kare muhalli tamkar wani yunkurin dankwafar da ci gaban kasashen na Afrika lura da yadda kacokan tattalin arzikinsu ya dogara a bangaren makamashin da suke tonowa kama daga Iskar gas da man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.