Isa ga babban shafi

Taron Brics: Zamu gudanar da taron mu keke da keke- Cyril Ramaphosa

Shugaban kasar Africa ta Kudu Cyril Ramaphosa ya jadadda cewa taron shugabannin kungiyar kasashen BRICS da tattalin arzikin su ke tasowa zai kasance na keke da keke duk kuwa da bukatar kama Shugaban kasar Russia Vladmir Putin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta aikewa Africa ta kudu da zarar ya Sanya kafar sa a kasar.

Президент ПАР Сиріл Рамафоса та президент РФ Володимир Путін. Саміт Росія Африка, Сочі, жовтень, 2019
Президент ПАР Сиріл Рамафоса та президент РФ Володимир Путін. Саміт Росія Африка, Сочі, жовтень, 2019 AP - Sergei Chirikov
Talla

Duk da dai shugaba Ramaphosa bai fito karara ya bayyana ko Putin zai halarci taron ko akasin haka ba, amma dai ya ce taron nasu ba wanda za’a gudanar da shi ta yanar gizo bane.

Duniya ta dade tana jiran watan Agusta, lokacin taron wadannan shugabanni don ganin yadda zata kaya da Mista Putin, wanda kotun ke bukatar Africa ta kudu ta kama shi ta kuma mika mata shi da Zarar ya Sanya kafar sa a kasar don hukunta shi, bisa zargin cin zarafin yara da kuma korar yaran Ukraine daga kasar sa ba bisa ka’ida ba.

Tuni dai kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ajiye wakilin ta wanda zai kama shugaba Putin cikin shirin ko ta kwana.

Akwai dai jita-jitar da ke cewa shugabannin kungiyar zasu mayar da gudanar da taron kasar China, amma kalaman na Mr Ramaphosa basu tabbatar da karyata hakan ba, illa dai yace a wannan karo za’a gudanar da taron ne keke da keke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.