Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 10 na fama da yunwa a yammacin Afrika - MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 10 ne ke fama da tsananin yunwa da ba a taba  ganin irin ta ba a yammacin Afrika, ba kuma tare  da samun taimako daga kowanne bangare ba. 

Wata uwa na shayar da danta ruwa
Wata uwa na shayar da danta ruwa Rachel Palmer
Talla

A cikin wani rahoton bincike da hukumar ta fitar ta ce fiye da rabin adadin mutane miliyan 11 da dubu 600 da aka yi hasashen za su yi fama da tsananin yunwa ba su sami tallafain da ya kamata ba. 

Hukumar ta alakanta hakan da karancin kudi da take fama da shi da kuma tashe-tashen hankali da mafi yawan kasashen yankin ke fama da su. 

Rahoton hukumar ya ci gaba da cewa akwai bukatar a yi gaggawar samar da kudaden da za ta ci gaba da aikin fatattakar yunwa a irin wadannan kasashe, matukar ba haka ba kuma, karin wasu dubban daruruwa na cikin barazanar fadawa yunwar mai tsananin da ba  a taba ganin irin ta ba. 

A kiyasin da hukumar ta yi, ta gano cewa akalla mutane miliyan 27 a kasashen yammacin Afrika ne ke fama da tsananin yunwa, tun ma kafin bullar cutar Korona, barkewar rikicin Ukraine da Rasha da ma mummunar ambaliyar da kasashen suka rika fuskanta a bara. 

Baya ga adadin mutanen da ke bukatar agajin gaggawa game  da yunwar akwai kuma wadanda suke bukatar dauki amma ba na gaggawa ba da adadinsu ya zarce miliyan 47 mafi yawansu mata da kananan yara a cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.