Isa ga babban shafi

MDD ta kadu da cin zarafin da ake yi wa mata a Sudan

Manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana kaduwa dangane da karuwar cin zarafin mata manya da yara a Sudan, yayin da aka shafe kusan watanni 3 ana gwabza kazamin fada a kasar tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar.

Wasu matan Sudan da ke zanga-zanga a birnin Khartoum
Wasu matan Sudan da ke zanga-zanga a birnin Khartoum RFI
Talla

 

Sanarwar hadin gwiwa da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka fitar, ta ce ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar a Sudan ya samu sahihan rahotanni na cin zarafi tare da yi wa mata akalla 57 fyade har sau 21 tun bayan barkewar rikicin Sudan a tsakiyar watan Afrilu. 

Rahoton masu binciken ya kara da cewar a cikin wani hari guda da aka kai yayin rikicin na Sudan sai da aka yi wa mata kusan 20 fyade. 

Tun kafin barkewar rikicin Sudan, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar mata manyansu da kanana miliyan 3 ne ke fuskantar barazanar nau’ikan cin zarafi a kasar ciki kuwa har da fyade.  

A baya bayan nan ne kuma majalisar dinkin duniyar  ta  ce adadin matan na Sudan da ke fuskantar barazanar cin zarafin ya karu zuwa kimanin miliyan 4 da dubu 200 daga mata miliyan 3. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.