Isa ga babban shafi

Ana ta luguden wuta a sassan birnin Khartoum

Ana gwabza mummunan fada a sassan birnin Khartoum na Sudan a wannan Talatar, inda har aka kakkabo wani jirgin yakin sojin kasar, yayin da ake ci gaba da harbe-harben makaman atilari da bindiga mai sarrafa kanta kamar yadda rahotanni ke cewa.

Hayaki da ke tashi a wasu sassan Khartoum babban birnin kasar Sudan yayin fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF da suka bijire.
Hayaki da ke tashi a wasu sassan Khartoum babban birnin kasar Sudan yayin fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF da suka bijire. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Wani mutun da lamarin ya faru a gaban idonsa ya bayyana cewa, sun hangi matukan jirgin yakin da aka kakkabo suna durowa daga sararin samaniya rike da sojan lema a daidai lokacin da jirgin ya kusan faduwa kasa.

Wata majiya ta ce, dakarun Rapid Support Forces ne suka harbo jirgin tare da cafke daya daga cikin matukansa jim kadan da durowarsa kasa.

A wani labarin kuma, an bada rahotan fase-fashen abubuwa a birnin na Khartoum a jiya Litinin a daidai lokacin da sojin gwamnatin kasar ke ta rokon fararen hula da su dauki makamai domin taimaka musu wajen tunkarar dakarun RSF.

Sai dai fararen hular sun yi watsi da wannan kira na su ma su shiga yakin, inda suka ce bukatarsu ba ta wuce a kawo karshen fadan da ake gwabzawa ba.

Kimanin mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da aka fara yakin a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata, yayin da likitoci ke cewa, akwai yiwuwar alkaluman mamatan sun zarta haka.

Kazalika akwai mutane miliyan 2 da dubu 2 da suka rasa muhallansu a sanadiyar yakin a cikin kasar ta Sudan, sannan dubu 645 sun fice daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.