Isa ga babban shafi

Ghana za ta karbi 'yan gudun hijirar Burkina Faso

Hukumomin Ghana na shirye-shiryen karbar ‘yan gudun hijirar Burkina Faso kimanin dubu 4 domin tsugunar da su a wani sansani da ke can yankin gabashin kasar.

Ghana ta gina sansanin 'yan gudun hijira mai daukar nauyin mutane dubu 4
Ghana ta gina sansanin 'yan gudun hijira mai daukar nauyin mutane dubu 4 © Nipah Dennis, AFP
Talla

Ghana za ta gudanar da wannan aikin na jin-kai ne tare da taimakon Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, inda ta ce, ba za tsugunar da mutanen na Burkina Faso ba a kan iyaka saboda dalilai na tsaro.

Da ma dai ‘yan gudun hijirar na Burkina Faso sun kwashe tsawon watanni suna tururuwa cikin Ghana domin neman mafaka sakamakon hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai musu a kasarsu.

Yanzu haka jami’an Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin na Ghana sun hallara a yankin gabashin kasar domin ci gaba da shirye-shiryen tsugunar da ‘yan gudun hijirar a sansanin da aka kaddamar da shi a  cikin watan jiya wanda ke daukar nauyin mutane dubu 4.

Hukumomin na Ghana da jami’an na Majalisar Dinkin Duniya na ta kokarin shawo kan ‘yan gudun hijirar da suka nuna turjiya kan cewa, su fa ba za su nausa can cikin kasar Ghana ba, inda suka fi gamsuwa da a zaunar da su a kan iyakar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.