Isa ga babban shafi

Cututtuka da yunwa sun mamaye Khartoum na Sudan

Cututtuka da tsananin yunwa sun fara tasiri a birnin Khartoum na Sudan bayan da rikici ke kara rincabewa a tsakanin bangarori biyu da ke yaki da juna, yayin da adadin masu tserewa daga muhallansu ke kara yawa.  

Wasu mazauna Sudan yayin kokarin ficewa daga kasar don gujewa fadan da ake gwabzawa tsakanin rundunonin dakarun kasar biyu.
Wasu mazauna Sudan yayin kokarin ficewa daga kasar don gujewa fadan da ake gwabzawa tsakanin rundunonin dakarun kasar biyu. REUTERS - EL TAYEB SIDDIG
Talla

Wasu mazauna Khartoum sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, luguden wuta ta cikin jiragen yaki ne ya farkar da su daga barci, abin da ke kara alamta irin munin da yakin ya yi.   

Kawo yanzu an kai wa ofisoshin ‘yan sanda a birnin Khartoum da dama hari yayin da luguden makamai mai linzami ya tarwatsa ginin kafar talabijin din kasar.  

Ta cikin wata sanarwa da rundunar RSF ta fitar, ta dauki alhakin kadddamar da hare-haren, duk da dai har yanzu gwamnati ba ta mayar da martani game da wannan lamari ba. 

Kawo yanzu mazauna birnin na Khartoum na ganin yakin bai taba munin da ya yi a yanzu ba, kasancewar dakarun na gwabzawa ne yanzu haka a tsakiyar birnin. 

Duk da cewa dakarun RSF ne ke mamaye da birnin na Khartoum, amma ana zargin su da sace kayan jama’a da shigewa gidajen wadanda suka tsere. 

Wannan al’amari ya tilasta wa shugaban gwamnatin sojin kasar, Abdelfatah Al-Burhan rokar matasa da su shiga aikin soja don tunkarar dakarun na RSF. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.