Yunwa ta kashe mutane a Habasha saboda rashin tallafi
Yunwa ta kashe daruruwan mutane a yankin Tigray bayan da Majalisan Dinkin Duniya da kasar Amurka sun dakatar da tallafin abincin da suke bai wa kasar Habasha.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya da Amurka tun farko sun dakatar da tallafin ne a watan Maris bayan da suka gano kumbiya-kumbaya da ake yi na sace abincin da aka tanadar don mabukata.
Sai dai sun kara tsawaita dakatarwar zuwa wasu sassan Habasaha a watan Yuni, hakan ya shafi mabukata miliyan 20, wato kashi daya bisa shida na yawan al'ummar kasar.
Hukumar Jin Kai ta samu rahotanin mace-mace na mutane 728 da ke da alaka da yunwa a uku daga cikin yankuna 7 tun bayan da aka dakatar da tallafin abincin a watan Maris.
Wannan jawabi wanda kawai hukumomin gundumomi suka tattara ne, kamar yadda shugaban Hukumar Jin Kai ya tabbatar.
A tsakiyar watan Maris hukumomin bada tallafi na Amurka suka gano abincin tallafi na akalla mutane dubu 134,000 ana sayar wa a kasuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu