Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta yi alkawarin lada mai tsoka ga wanda ya kamo mata wasu 'yan ta'adda

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta yi alkawarin bayar da kyautar dala dubu 300, ga duk wanda ya taimaka mata da bayanan da za su kai ga cafke wa, ko kuma halaka manyan ‘yan ta’addan da suke jerin wadanda take nema ruwa a jallo. 

Shugaban gwamnatin sojan Burkina Faso Ibrahim Traore, daga tsakiya
Shugaban gwamnatin sojan Burkina Faso Ibrahim Traore, daga tsakiya AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

A ranar Alhamis ne dai jami’an tsaron Burkina Faso suka wallafa sunayen ‘yan ta’adda 20 da suka ce za a bayar da kyautar ta dala dubu 300, kwatankwacin CFA miliyan 100 akan kowannensu. 

Daga cikin wadanda ake farautar akwai Sidibe Dramane mai shekaru 45, wanda ake yi wa lakabi da Hamza, sai kuma Diallo Moussa mai shekaru 40 da ake yi wa lakabi da Abou Ganiou. 

Bayanai sun nuna cewar Sidibe Dramane, sanannen abokin Amadou Koufa ne dan kasar Mali da ke jagorantar kungiyar GSIM mai alaka da Al-Qaeda. 

Dukkanin ‘yan ta’addan da ke cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo haifaffun kasar Burkina Faso ne akasarinsu kuma daga arewacin kasar, idan aka dauke Sita Housseini, mai shekaru 33 dan asalin Jamhuriyar Nijar. 

Alkaluman da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar sun nuna cewar, fararen hula da sojoji da 'yan sanda fiye da dubu 10,000 ne suka rasa rayukansu a hare-haren ‘yan ta’addda masu ikirarin jihadi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.