Isa ga babban shafi

Tasirin tawagar Afrika wajen sasanta rikicin Rasha da Ukraine

Sanarwar shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa  kan aniyar tura wata tawagar Afrika  kan neman zaman lafiya a Ukraine da Rasha ta baiwa jami’an diflomasiyar Afrika da dama mamaki, domin nauyin shiryata da daukar nauyi duk, sun ratayu ne a wuyan  wata gidauniyar kasar Brazil, da wani bafaranshe ya kafa, ya ke kuma jagoranta cewa da, Jean-Yves Olivier. 

Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine.
Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine. REUTERS - STRINGER
Talla

Sanarwar da Cyril Ramaphosa ya yi, a ranar talata 16 ga watan mayu na shekarar ta 2023 miladiya. A cewar shugaban kasar Afrika ta Kudu, biranen Kiev da Mosko sun bayyana amincewarsu da yi wa tawagar ta nahiyar Afrika karkashin jagorancin shugabanin kasashen  Zambiya, Senegal, Congo-Brazzaville, Uganda, Masar da kuma Afrika ta kudu. 

To sai dai tun lokacin shiru kake ji. Sai dai kuma tuntubar da RFI ta yi wa wasu manyan jami’an kasashen da abin ya shafa, ba mai son ya ce uffan a halin yanzu.  «a cikin irin wannan tattaunawa, yin wani tsokaci na  iya dagula komai», a cewar wani minister.  

Ke nan a daura da hurumin diflomasiya kamar yadda aka saba ne aka tsara wannan tawaga. Daga cikin huldar   shuwagabanin kasashe ne, wannan Gidauniya ta kasar Brazil, da aka kafa a 2015 da kuma bafaranshe Jean-Yves Ollivier ke jagoranta. Attajiri da ya samu dukiyarsa ta hanyar shiga tsakani wajen tattauna cinakayar danyar haja a ko ina cikin duniya, musaman a nahiyar Afrika, inda yau da shekaru da dama  ya saka kafaffar hudda da masu mulkin nahiyar Afrika. 

 Tun daga tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Félix Houphouët-Boigny zuwa ga shugaban kasar Congo-Brazzaville Denis Sassou-Nguesso ka zarce ka tabo shugaban Angola José dos Santos, Jean-Yves Ollivier sananne ne ga fadodin shuwagabanin kasashe.  a shekarar 2014 ya yi wata fira da RFI inda daga ciki ya ke cewa : «Na mayar da hankali kan harakoki amma ga shi siyasa ta kama ni»,  

Boyayyen Jarumi   

Makusanci ne ga shugaban Faransa marigayi Jacques Chirac, Jean-Yves Olivier ya yi aiki ne a Afrika ta kudu, a lokacin mulkin nuna wariyar launin Fata da ma lokacin  Nelson Mandela, Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Comoros ko kuma kasar Soudan. A shekarar ta 2020 a birnin Lome na kasar Togo ya shirya wani taron mahawara kan yaki da magungunan Jabu, a gaban shuwagabanin kasashen Afrika guda 7. « Mun san a  yau safarar miyagun kwayoyi ta ciyar da kowa rashawa, kama  tun daga kasa, har zuwa kololuwar kasa, wanda kuma hakan ke rayar da  ta’addanci», a cewar Jean-Yves Olivier a jawabin rufe zaman taron da ya gabatar. 

Shine yanzu kuma,  gidauniyarsa da ya kafa, da kuma ta kirkiri yinkuri tawagar neman zaman lafiya ta  Afrika da shugaba Cyril Ramaphosa ya kaddamar. Ta hanyar hada yinkurinsa  da shuwagabanin nahiyar Afrika shida, Jean-Yves Ollivier ya karya harufan sirrin diflomasiya, tare da tunkarar wani babban kalubalen duniya.  Idab shugaban Rasha  Vladimir Poutine da  Volodymyr Zelensky na Ukraine sun amince da wannan shawara ta sa yanzu abu mafi wuya shine shirya tawagar. 

Yanzu kuma ya kamata a kaddamar da sabuwar tattaunawa, domin tsaida lokaci na bai daya tsakanin shuwagabanin kasashen na Afrika 6 da kuma shugaba Putin da Zelenski. Bayanan da ke zo mana na bayyana cewa, wannan tawaga ta neman zaman lafiya a shirya ta ne a kan kwanaki 4 a karshen watan Yuni a matsayin lokacin da aka tsaida. Tabbaci guda : Idan komai ya tabbata, tawagar zata fara ne da farko da Kiev kafin ta wuce Mosko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.